Like Us On Facebook

Breaking

Friday, April 5, 2019

Hotunan Abba Kyari a lokacin da yake neman masu garkuwa da mutane a dajin Kaduna


Babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna ta zama matattarar 'yan fashi da masu garkuwa da mutane, inda mutane da dama suke tsoron bin hanyar sanadiyyar kama mutane da 'yan garkuwa da mutane suke yi.

Hakanne ma ya sanya hazikin dan sandan nan Abba Kyari tare da tawagar sa suka shiga dajin dake kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna din domin kama masu garkuwa da mutanen, akwai yiwuwar shigar Abba Kyari dajin zai iya sanyawa a samu saukin 'yan ta'addar da suke damun al'umma, saboda ganin irin hazakar da dan sandan yake da ita.




Idan ba a manta ba a jiya Laraba 3 ga watan Afrilu, majiyarmuLEGIT.NGta kawo muku yadda gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufai da tawagar sa suka tarwatsa wasu 'yan ta'adda da suka yi kokarin garkuwa da matafiya akan hanyar ta Abuja zuwa Kaduna.



Rahoton hakan ya fito daga bakin wani na hannun daman gwamnan Samuel Aruwan, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai.
Aruwan ya bayyana cewa, a lokacin da suke kan hanyar su ta zuwa Abuja, gwamnan ya yi kicibus da motoci a tsaye akan hanya, kusa da kauyen Akilubu, da misalin karfe 3:40 na yammma. Ya kara da cewa mazauna kauyen sun bayyana cewa akwai masu garkuwa da mutane da suka tare hanyar.




A sanarwar ta sa ya bayyana ce wa:"Jami'an tsaron da suke tawagar gwamnan sune suka je suka kori 'yan ta'addar, suka arce cikin daji.
"Bayan tawagar ta kori 'yan ta'addar, gwamnan ya bada umarnin a dauki mutanen da 'yan ta'addar suka yi wa rauni a kai su asibiti mafi kusa.
"Sannan gwamnan ya bukaci jami'an tsaro su, tsaya domin tabbatar da hanyar ta yi lafiya ga matafiya."


Source: Hausa.legit.ng

No comments:

Post a Comment