Like Us On Facebook

Breaking

Thursday, May 28, 2020

Ane Neman Dr. Zakeer Naik Ruwa A Jallo

ME YASA SUKE SON SU KASHE DR. ZAKIR NAIK?
Bangiskhan
Waye wannan Dr Zakir Naik din?
.
TAKAITACCEN TARIHIN RAYUWARSA
.
Cikakken sunansa shine Zakir Abdulkareem
Naik.
An haife shi a ranar 18 Oct. 1965 a birnin
India
na Mumbai a Maharashtra.
Zakir ya hallaci makarantu da dama inda ya
samu shaidar zama likitan tiyata wato
"Bachelor
of Medicine and Surgery".
Zakir Naik na tare da mai dakinsa Farhat
Naik, da
kuma 'yaya biyu Fariq Naik da Rushdaa Naik.
.
Zakir Naik ya tsinci kansa cikin sahun masu
Da'awah a shekarar 1991, lokacin da
Muslunci ya
tsinci kansa cikin tsangwama da muwiyacin
hali a
kasar India saboda gallazawar da masu
addinin
Hindu kewa Muslunci da Musulmi.
Zakir ya tasirantu ne da salon da'awar
sannanen
malam nan wato Sheikh Ahmad Deedat
wanda
Zakir ya hadu dashi a shekarar 1987, kamar
yadda Naik na sheda a 2006, saboda tarin
baiwa
ta ilimi da Allah yayiwa Zakir yasa Deedat da
kansa yake masa lakabi da "Deedat-Plus"
wato
kamar kace, "Malam da rabin Malam".
.
RUGUZA MASALLACIN BABRI
.
A shekarar 1992 wani muhimmin al'amari
ya faru.
A ranar 6, ga watan Disamba, na shekarar
1992,
masu bin addinin Hindu kimanin 150,000 da
taimakon jam'iyun siyasa na India; Bharatya
Janata Party (BJP) da Vishva Hindu Parishad
(VHP) suka afkawa gami da rugurguza
Masjid
(masallacin) Babri mai dadden tarihi a cikin
garin
Ayodhya bayan haka suka ruguje masallatai
masu
yawa a yankin, masallacin Babri an gina
shine tun
qarni na 16 kimanin shekaru 500 da suka
wuce.
Rushe masallacin ya jawo gagarumar riga
wadda
tayi sanadiyar asarar dukiyoyi masu tarin
yawa
da kuma mutuwar mutane fiye 2,000
wadanda
yawancinsu Musulmi ne.
.
Hakika wannan rigima ta kara jefa
Musulman
India cikin halin ha'ula'i, zullumi da kaskanci,
suka zamo basu da wata ta cewa, Muslunci
ya
zama abin zolaya gami da tsokana.
Ana cikin wannan hali ne, Allah yayi nufin
dawo
da martabar Muslunci da Musulmi ta hannun
Sheikh Dr. Zakir Naik, kamar yadda
Muhammad
Reyaz ya sheda.
.
# DEBATES DINSA
.
Dr. Zakir ya fara mahawararsa (debate) ta
farko
a 1994 kan wani littafi mai suna "Lajja"
wanda
wata mashahuriyar mai aibata muslunci
Taslima
Nasreen 'yar kasar Bangladesh ta wallafa.
Haka a shekarar 2000, Zakir yayi mahawara
da
sanannen masanin kimiyar nan Dr. William
Campbell a birnin Chicago ta Amurika.
Campbell
ya kwashe shekaru yana nazari kafin daga
bisani
ya wallafa wani littafi da yace Qur'an yaci
karo
da kimiyar zamani (modern science).
Muhawarar
mai taken "The Qur'an and the Bible in the
Light
of Science" ta daukaka Naik saboda yadda
yayi
kaca-kaca da littafin da aka dau shekaru ana
wallafa shi da hujja cikin kankanin lokaci,
hakan
yasa Zakir ya zama abin tsoro tsakanin masu
yiwa Muslunci zambo, kamar su Ali Sina
wani dan
asalin Iran mai tsananin adawa da Muslunci.
.
Zakir Naik wanda zaka iya kwatanta
kwakwalwarsa data "computer" saboda
kaifin rike
abu, ya gudanar da lakcoci kusan 4000 a
fadin
duniya baki daya wanda ya hada da
zuwansa
Nigeria har sau biyu.
.
NASARORINSA
.
A bisa kokari irin nasa Zakir ya samar da:
i, tashoshin satellite na Peace TV English,
Peace
TV Bangla, Peace TV Urdu da kuma Peace TV
Chinese. Tashoshin wadanda babu kamar su
wajen yada addini, kimanin mutane miliyan
150
ne suke iya kama Peace TV a kasashe fiye da
200.
Zakir Naik ya samar gami da jagorantar;
ii, "Islamic Research Foundation" (IRF) wato
cibiyar bincike ta addinin Muslunci, a
karkashin
IRF aka samar da (IIS) wato "Islamic
International
School".
iii, Sai kuma (UIA) "United Islamic Aid"
wadda
aikinta shine bada tallafin karatu ga
nakasassu
da masu rauni.
.
Irin wannan nasarori da Zakir Naik ya samu,
gami
da dawo da martabar Musulmai a India
dama
duniya baki daya, sune suka tsone idanun
munafukai musamman masu son gani
bayan
Muslunci, tako wace fuska.
.
Gazawar masu son ganin bayan Muslunci a
sakamakon Zakir, yasa suke kokarin ganin
bayansa, ta hanyar tsomashi cikin ayyukan
ta'addanci, zargin da ako yaushe yake
musawa
.
Karku manta jam'iyar Bharatya Janata Party
(BJP) wacce ta taka rawa wajen gallazawa
Musulman India itace ke mulki yanzu. Kuma
Prime Minister na yanzu Narendra Modi
babban
yaron Lal Krishna Advani ne, wanda ya
jagoranci
ruguza masallatan Ayodhya a 1992. Saboda
haka
babu mamaki cikin sabon salon rufe bakin
Musulmai ta hanyar gamawa da Zakir Naik a
farko.
.
MUSULMAI MASU ADAWA DASHI
.
Yawancin masu adawa Zakir Musulmai 'yan
Shi'a
ne, suna zarginsa da rashin yin biyayya ga
dokokin zamantakewa na India daga
cikinsu
akwai:
Kalbe Jawad Naqvi da kuma Yasoob Abbas
dss.
Amma yawancin qungiyoyin musulmai na
mara
masa baya kamar su: Sheikh Abdulkadir
Jilani
Foundation, Darul Uloom da kuma All-India
Sunni
Board.
.
BARAZANA GA RAYUWARSA
.
A ranar 13 ga watan Juli 2016 shugabar
Vishva
Hindu Parishad (VHP) wato Sadhvi ya bada
sanarwar bada tukyici na dalar Amurika
$78,000
ga duk wanda ya fillo kan Zakir Naik. Hakan
yazo
kwana daya bayan wata kungiyar Shi'a
maiwa
kanta laqbi da Hussaini Tigers. ta sanya
ladan
$23,000 ga wanda ya kashe Zakir Naik.
.
DAUKAKARSA
.
Zakir ya sami zama mutum na 89 cikin
mutane
100 dake da karfin fada aji a India kasar
dake da
mutane fiye da biliyan daya da miliyan dari
uku.
(1.3 bn) ya sake zama na 82 a shekarar
2010
kamar yadda The Indian Express ta sanar.
.
Yanzu haka yana gudun hijra a kasar da
ba'a
gano ba.
Allah ya kareshi ya karowa Muslunci
wadanda
suka fishi ameen.

No comments:

Post a Comment