Like Us On Facebook

Breaking

Saturday, September 5, 2020

An zargi sojojin ƙasar da kashe fararen hula 70


 Ana zargin an yi kashe-kashen ne a farkon wannan shekarar


Hukumar kare haƙƙin ɗan Adam ta Jamhuriyyar Nijar ta zargi sojojin ƙasar da kashe gwamman fararen hula a yayin wasu hare-hare na ƙoƙarin daƙile harin ta'addanci.


Ta ce ta gano fiye da gawarwaki 70 a wasu manyan ƙaburbura shida a Tillaberi da ke arewa maso yammacin ƙasar, wani yanki da hare-haren masu tsattsauran ra'ayi ya shafa.


Ana zargin an yi kashe-kashen ne a farkon wannan shekarar.


Ɗaya daga cikin masu binciken ya ce an kashe fararen hular ne da makamai irin su takobi da adduna da kuma wasu ƙananan makaman.


Ƙungiyoyin kare hakkin ɗan Adam na duniya sun zargi sojojin Nijar da Mali da kuma Burkina Faso da kashe gwamman mutane ba bisa ƙa'ida ba a yayin da suka kai wa masu ayyukan ta'addanci hare-hare a yankin Sahel.


Hukumar kare hakkin ɗan Adam ta Nijar tana bincike kan zarge-zargen cewa fararen hula 102 sun ɓata a yankin da ke fama da rikici tsakanin 27 ga watan Maris zuwa 2 ga watan Afrilu bayan wani harin sojoji.


"Tabbas an kashe fararen hula kuma an gano gawarwakin aƙalla 71 a wasu manyan ƙaburbura,'' a cewar Abdoulaye Seydou, shugaban wata cibiya ta kawo zaman lafiya da cigaban dimokraɗiyya a Afrika, wadda da hannunta cikin binciken.


Ya ƙara da cewa: "Akwai hannun Rundunar Dakarun Tsaro ta (FDS) kan waɗannan kashe-kashe.''


Amma Mr. Seydou ya ce ba zai yiwu a faɗi ko da hannun manyan sojoji a ciki ba.


Har yanzu babu wani martani daga hukumomin Jamhuriyyar Nijar kan zargin

No comments:

Post a Comment