Like Us On Facebook

Breaking

Wednesday, September 2, 2020

Kimiyyar Lantarki a Sawwake (1)

A yau za mu fara bincike na musamman kan abin da ya shafi kimiyyar lantarki da yadda makamashin lantarki ke samuwa, duk a mahangar kimiyya. Wannan shi ne kashi na daya mai dauke da mukaddima. A sha karatu lafiya.


A yau cikin yardar Allah ga mu dauke da maudu’i na musamman kan fannin kimiyyar lantarki; wani fannin da bamu taba yin bincike a cikinsa ba, duk da mahimmancinsa ga rayuwar al’umma da tattalin arzikinsu. Rubutu kan wannan fanni na lantarki zai dauke mu wasu makonni nan gaba. A yau zamu yi bayani ne kan mahimmancin wannan fanni, bayan takaitaccen bayani daga asalinsa. Sannan muyi bayani kan madaukan lantarki; ma’ana: mahallin da lantarki ke gudanuwa kenan. A gaba mu kawo bayanai kan nau’ukan sinadaran lantarki. Sai kuma bayani kan yadda sinadarin maganadisun lantarki ke gudana a mahallinsa. Daga cikin bincikenmu har wa yau, mai karatu zai ci karo da bayani kan farantin makamashin lantarki, wanda a harshen Turanci ake kira: “Electrical Circuit.” Wannan faranti shi ne hakikanin abin da idan ka fahimce shi a ilimin lantarki, ka kusan kure fannin. Domin duk wata na’urar dake dauke da sinadarai ko makamashin lantarki a wannan zamani, tana dauke ne da wannan faranti. Kada in cika ku.


Daga cikin bincikenmu za mu kawo bayanai kan abubuwan da ake sarrafa su don samar da wutar lantarki a duniyar yau. Wannan zai zo ne bayan ‘yar takaitacciyar karatun tarihi da za mu yi kan asalin lantarki na zamanin da; tsakanin wanda ke samuwa daga sararin samaniya da wanda ke samuwa daga halittun dake rayuwa a teku. Za mu ci karo har wa yau da bayani kan tarihin lantarkin zamani; su wa da wa suka assasa wannan fanni a duniyar yau? Kasidar ba za ta kare ba sai masu karatu sun san yadda ake kididdige kima da yawan wuta ko makamashin lantarki dake gudanuwa a na’urorin sadarwa na zamani masu amfani da wutar lantarki. Wannan zai kaimu ga bayani kan ka’idojin ilimin kimiyya da wasu masana suka assasa don karantawa da nazarin wannan fanni a kimiyyance (Scientific Laws), irin su Ohm, da Fradays’ Laws. A karshe, masu karatu za su samu bayanai kan asalin kwan lantarki ko kayayyakin da ake amfani dasu wajen haska wutar lantarki a dakuna da gidaje da ma’aikatu ko masana’antu. Su waye suka samar dasu a asali?


Wadannan, a takaice su ne kadan daga cikin abubuwan da wannan maudu’i namu zai kunsa in Allah ya so. A daya bangaren kuma, bazan yi magana a kan matsalolin wutar lantarki a Najeriya ba. Don haka, kada a rubuto mini tambaya kan wannan maudu’i. Kasidar za ta mayar da hankali ne kan fannin a ilimance, da nazarce. Manufar hakan kuwa ita ce ne don yada ilimi, ba muhawara cikin siyasar samar da wutar lantarki ba a Najeriya. Da fatan za a kiyaye wajen aiko tambayoyi ko tsokaci.

A tare mu a gaba
 

No comments:

Post a Comment