Like Us On Facebook

Breaking

Friday, September 4, 2020

Muhammadu Buhari: PDP ta ce gwamnatin APC ta jawo ƙunci da talauci

 

Ƴan Najeriya na ƙoƙawa da halin da gwamnatin Buhari ta jefa su


Babbar jam`iyyar hamayya a Najeriya wato PDP ta yi zargin cewa da gangan gwamnatin Shugaba Muhamadu Buhari ta ƙara farashin man fetur da wutar lantarki domin ta ƙuntata wa al`umma.


A wannan makon ne kamfanin mai da hukumar wutar lantarki suka sanar da ƙarin farashin. Sai dai jam`iyyar APC ta musanta, ta na cewa PDP ce silar matsalolin ƙasar.


PDP ta yi zargin cewa ƙeta ce tsagwaro a zuciyar jam`iyyar APC mai mulki, kuma wannan ne ya sa ta ninka farashin man fetur da na wutar lantarki ba tare da la`akari da irin mawuyacin halin da `yan Najeriya suka samu kansu a ciki ba.


Jam'iyyar hamayyar ta ce ko farfaɗowa ƙasar ba ta yi ba daga bugun da annobar korona ta yi ma ta.


Sakataren yaɗa labaran jam`iyyar mista Kola Olagbondiyan ya shaida cewa bukatar su ita ce a gaggauta soke ƙarin farashin da aka yi, don kauce wa jefa ƙasa cikin rikici.


Ya ce: ``Jam`iyyar mu na da yaƙinin cewa ƙarin farashin litar mai da aka yi, daga naira 87 a zamanin mulkin PDP a shekara 2015 zuwa naira 151 farashin dappo da wata manufa aka yi, sannan bugu-da-ƙari aka kara farashin kudin kilohat guda na wutar lantarki daga naira 30 zuwa naira 62.


''Jam`iyyar APC ta kau da dukkan shakku cewa tana aniyar gana wa `yan Najeriya azaba, don cimma wata manufarta ta son zuciya.''


Jam`iyyar PDP ta ce duk mai lissafi ya san dangantakar da ke tsakanin rayuwar al`umma da wutar lantarki da man fetur, don haka duk lokacin da farashinsu ya hau, to babu makawa sai talakawa sun galabaita. Kenan babu gwamnatin da ke tausayin jama`a da za ta kau da kai ga irin wannan hauhawar farashin!


Ganin cewa mai ba wata tsada can yake yi a kasuwar duniya ba, jam`iyyar PDP ta ce ba ta san da wane mizani gwamnatin Najeriyar ta yi amfani da shi wajen kara farashin man ba, saboda haka ya kamata ta fito ta yi bayani.

No comments:

Post a Comment