
Shugaban ya bayyana cewa an kwato kadarori da kuma kudade a yaki da ake yi da cin hanci da rashawa.
A bangaren tattalin arziki, ya bayyana cewa an samu ci gaba wajen samar da abinci a Najeriya ta hanyar inganta noma da kuma hana fasa kwaurin shinkafa.
Sai dai ya bayyana rashin aikin yi a matsayin matsala a kasar ganin cewa kashi 60 cikin 100 na 'yan kasar matasa ne.
Tsohon gwamnan jihar ta Akwa Ibom Sanata Godswill Akbabio shi ne shugaban yakin neman zaben na Shugaba Buhari.
Hakan ne ma ya sa ake ganin cewa an zabi jihar ta Akwa ibom ta zama jihar da za'a kaddamar da yakin neman zaben.
Duk da cewa jamiyyar adawa ta PDP ce ke da iko a jihar, Sanata Akpbabio dan siyasa ne mai karfin fada a ji wanda kuma yake da tasiri a harkokin siyasar jihar.
Wannan dai shi ne yakin neman zabe karo na 5 da Shugaba Muhammadu Buhari zai yi a Najeriya.
A 2003 ya yi yakin neman zabe tare da Chuba Okadibo a matsayin mataimakin sa.
Haka a 2007 ya yi yakin neman zaben tare da Edwin Ume-Ezeoke.
A 2011 ya fito tare da hon. Tunde Bakare a matsayin mataimaki.
A zaben 2015 kuma tare da Prof. Yemi Osibanjo wanda a lokacin ne ya yi nasarar lashe zaben.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da yakin neman zabensa a garin Uyo dake jihar Akwa Ibom.
Shugaban ya yi jawabi ga tarin mutanen da suka hallara a filin wasa na garin.
Shugaban ya yi babban bayani kan tsaro inda ya tabbatar da cewa kungiyar Boko Haram bata rike da gari ko daya a halin yanzu a Najeriya, don haka gwamnatinsa ta yi nasara a kan kungiyar.
Shugaban ya bayyana cewa a lokacin da ya karbi mulki a 2015, Boko Haram na rike da kananan hukomi kusan 17 a jihohin Barno da Yobe, amma a halin yanzu ba ta da iko da ko daya.
Ya ce gwamnatinsa za ta cigaba da tabbatar da tsaro da habbaka tattalin arziki da kuma yaki da cin hanci da rashawa.
No comments:
Post a Comment