Bismillahir Rahmanir Rahim
Ya ku ‘yan uwana masu girma, masu daraja! Ku sani, yana daga cikin biyayya da kyautatawa iyayen mu, da hakkinsu a kan mu bayan Allah ya karbi rayuwarsu, mu kasance muna:
1. Nema masu gafarar Allah da yi masu Istighfari
Ya ku ‘yan uwana! Wajibi ne mu yawaita nema wa mahaifanmu gafara a wajen Allah a lokacin da suke raye, sannan mu kara nema masu gafara da yi masu istighfari kowane lokaci, mai yawa, bayan rasuwarsu.
Manzon Allah (SAW) yana cewa:
“Lallai Allah yana daukaka Daraja da matsayin mutum Salihi a cikin Aljannah, sai bawan yace; Ya Allah daga ina ne nike samun karin wannan daukaka da daraja? Sai Allah yace masa, saboda Istighfarin ‘ya’yan ka.” [Ahmad ne ya ruwaito shi]
2. Yi masu Addu’a
Wajibi ne ga kowane Da na kwarai, mai neman albarka, mai neman ya gama lafiya da duniya, ya rika yi wa mahaifansa Addu’a duk lokacin da zai roki Allah, kuma ya kara dagewa sosai da wannan Addu’ar a gare su bayan rasuwarsu.
Yana daga cikin alamar kai na kirki ne, kuma kai mai albarka ne, a same ka kana yawaita Addu’a ga mahaifanka.
Manzon Allah (SAW) yana cewa:
“Idan Dan Adam ya rasu, ladar ayyukan sa za su yanke sai guda uku kawai; Sadakar da yayi mai gudana, ko ilimin da ya koyar ake amfanuwa da shi, da Da na kwarai da zai rika yi masa Addu’a.” [Muslim ne ya ruwaito shi]
3. Biya masu dukkanin bashin da ke kansu
Bashi kala biyu ne kamar yanda Manzon Allah (SAW) ya bayyana:
– Bashi mafi girma shine bashin Allah.
– Bashi mai girma shine bashin dake tsakanin mutum da mutum.
Dukkan wadannan basussukan hakki ne na mahaifanmu a kan mu da mu sauke masu shi bayan rasuwarsu.
Manzon Allah (SAW) yana cewa:
“Ran mumini idan ya mutu ana kange shi daga isa zuwa ga rahamar Allah har sai an biya masa bashin da yake kan sa.” [Ahmad ne ya ruwaito shi]
Kuma Manzon Allah (SAW) yana cewa:
“Wanda yayi mutuwar Shahada (wato Shahidi) ana gafarta masa dukkan komai in banda bashin da yake kan sa.” [Muslim ne ya ruwaito shi]
Kuma Annabi (SAW) yace:
“…Bashin Allah shine yafi chanchanta da a biya masa.” [ Sahihul Jami’]
4. Cika bakancen su (Alwashi) da alkawuran da suka yi na alkhairi
Wajibi ne a biya masu bakancen su (Alwashi) da alkawuran su na alkhairi, kamar Azumi ko aikin Hajji ko Umarah ko wani daga cikin alkawura na alkhairi da suka yi.
5. Biya masu hakkin kaffarah da yake kan su
Kamar kaffarar kisan kai bisa kuskure ko kaffarar rantsuwa ko wanin wannan, to shima yana cikin hakkin mahaifa a kan ‘ya’yan su da su biya masu bayan rasuwarsu.
Wata mata tayi bakancen (Alwashin) za tayi azumi na wata guda, amma bata samu damar cikawa ba har ta rasu, sai ‘yan uwan ta suka zo wajen Manzon Allah (SAW) suka bashi labari, sai yace:
“Shin da ana binta bashi zaku biya mata? Sai suka ce Eh ya Manzon Allah, sai yace: To bashin Allah shine yafi chanchanta da a biya.” [Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi]
Da kuma matar nan da ta tambayi Manzon Allah (SAW) cewa:
“Mahaifiyata ta rasu ana bin ta bashin azumin wata guda, sai Annabi yace: Ki biya mata.” [Abu Dawuda ne ya ruwaito shi]
Kuma Manzon Allah (SAW) yace:
“Dukkan wanda ya rasu ana binsa bashin azumi to ‘yan uwansa su biya masa.” [Sahihul Jami’]
6. Kyautatawa yayyu, kanne da ‘yan uwan mahaifi da mahaifiya
Hakki ne na wajibi a kan mu mu kyautatawa ‘yan uwan mahaifanmu, kuma wajabcin yana kara karfi bayan rasuwarsu.
Manzon Allah (SAW) yace:
“Kanwa ko yayar mahaifiya tana da matsayin mahaifiya.” [Shaykh Albani a cikin Sahih Sunanu At-Tirmidhi]
Kuma Ibn Umar (RA) yace:
“Wani mutum yazo wurin Manzon Allah (SAW) yace: Ya Manzon Allah, Lallai ni na aikata wani zunubi mai girma, shin idan na tuba za’a amsa tuba na? Sai Manzon Allah (SAW) yace: Shin mahaifiyarka tana raye? Sai yace; A’a, sai Manzon Allah (SAW) yace: Shin kana da ‘yar uwar mahaifiya? Sai yace; Eh, sai Annabi (SAW) yace: To kaje ka kyautata mata.” [Shaykh Albani a cikin Sahih Sunanu At-Tirmidhi]
7. Sadar da zumuncin iyayen mu bayan rasuwarsu
Wajibi ne muci gaba da sadar da zumuncin iyayen mu bayan rasuwarsu, kamar girmama abokansu, da kai masu ziyara, da taimaka masu gwargwadon hali.
Daga Abi Buraidah (RA) yace: “Na iso garin Madinah, sai Abdullahi Bin Umar yazo ya same ni sai yace kasan dalilin da yasa nazo wurin ka? Sai nace a’a, sai yace: Naji Manzon Allah (SAW) yace: Dukkan wanda yake so ya sadar da zumuncin Baban sa alhali yana cikin kabari, to ya sadar da zumuncin ‘yan uwan Baban sa bayan sa, don haka nazo ne in sadar da zumuncin dake tsakanin Babana da Baban ka, domin abokan juna ne kuna ‘yan uwa ne.” [Ibn Hibban ne ya ruwaito shi]
8. Rama masu azumin da ake bin su
Idan azumin kaffarah ne ko na bakance (Alwashi) sune ake rama wa. Amma na Ramadan ba’a ramawa (wannan ra’ayin wasu malamai ne).
Manzon Allah (SAW) yace:
“Dukkan wanda ya rasu alhali ana binsa azumi, ‘yan uwan sa su rama masa.” [Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi]
9. Girmama abokan iyaye
Manzon Allah (SAW) yace:
“Yana daga cikin cikar biyayya ga iyaye, mutum ya sadar da zumuncin abokai da masoyan mahaifansa.” [Muslim ne ya ruwaito shi]
10. Yi masu Sadaka, ko yin Sadaka a madadin iyaye
Mafi alkhairin sadakar da zaka yiwa iyayen ka bayan rasuwarsu itace, sadaka mai gudana (Wato Sadaqatun Jariyah). Kamar gina Rijiyoyi, ko Boreholes ko Masallatai, ko Makarantu (na Islamiyyah da na zamani), ko daukar nauyin malamai masu karantar da al’ummah, sannan sai sadaka irin ta yau da kullum.
Amma sadaka wadda aka kebe mata lokaci da yanayi, muji tsoron Allah mu daina yin ta, domin wannan Bidi’ace. Misali, kamar sadakar uku ko sadakar bakwai, ko ta arba’in, ko ta shekara ko ta shekaru. Duk wadannan wallahi basu da wani dalili a cikin Addinin Musulunci. Kuma yin haka baya da Asali a Addini. Domin ba’a samu a ayyukan Manzon Allah (SAW) ba ko wani Sahabi ko wasu magabata na kwarai.
An karbo daga Sa’ad Dan Ubadata (RA), lokacin da mahaifiyarsa ta rasu sai yace: ya Manzon Allah, mahaifiyata ta rasu a lokacin bana kusa da ita, shin zan iya yi mata sadaka kuma ta amfane ta? Sai Manzon Allah (SAW) yace: Eh…” [Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi]
Don haka ba’a hana yiwa iyaye Addu’a ba, kai hasali ma wajibi ne yi masu Addu’a. Amma kebe mata lokaci, ko rana, ko wata ko shekara, wallahi wannan ba Musulunci bane, muji tsoron Allah mu daina, domin samun rahamar Allah.
Allah yasa mu dace. Allah ne mafi Sani.
Ina rokon Allah ya bamu ikon sauke nauyin iyayen mu da ke kan mu. Allah ya hada mu da su a Aljannah Firdausi, amin.
Dan uwan ku: Imam Murtadha Muhammad Gusau, daga Okene, Jahar Kogi, Nigeria. Za’a same shi a: gusaumurtada@gmail.com ko +2348038289761

No comments:
Post a Comment