A cikin watannin baya da suka shige idan masu karatu basu mance ba, mun gudanar da bincike na musamman kan hanyoyin ciyar da Najeriya gaba a fannin kimiyya da kere-kere. A wannan karo za mu dora da bayani kan hanyoyin ciyar da al’umma gaba a fannin kimiyya. Wannan shi ne kashi na daya.
Mabudin Kunnuwa
Daga tambayoyin da na amsa a kwanakin baya a wannan shafi mai albarka akwai tambayar Malam Ali Fancy dan mutan garin Garko, wanda ya nemi sanin ko gaskiya ne cewa masu aiki da na’urar gano cuta mai suna X-Ray Machine a asibiti ko dakin bincike, ba su yin tsawon rayuwa, sanadiyyar sinadaran da ke dauke cikin wannan haske na X-Ray mai dauke da guba mai cutarwa ga lafiya. Na bashi amsa ne ta hanyar kawo illolin da ke tattare da wannan haske, da bashi shawara don zuwa wajen likita da neman tabbaci kan zancen da yace ya ji a bakin wani likita da ke amsa tambayoyi a sashen Hausa na rediyon BBC.
Amma bayan wasu ‘yan kwanaki sai na lura cewa wannan amsa da na bashi, tare da wanda ya ji daga bakin wancan likita, na iya sa shi jin wata nakasa a cikin zuciyarsa. Ba shi kadai ba ma, har da ma duk wanda ya karanta wannan amsa. Wannan nakasa kuwa ita ce: ya ji cewa ashe wannan ba fannin da ya kamata a karanta ko a koya bane. Musamman ganin yadda muke da kasala a yau, wajen neman sauki da kauce wa mutuwa. Tabbas dabi’a ce mutum ya ji ba ya son mutuwa, amma duk yadda mutum ya kai da shiga hadari, sai kwanakinsa sun kare sannan zai mutu. Don haka na zurfafa tunani da bincike, don jaddada mana hanyoyin da za mu bi wajen ciyar da al’ummarmu gaba a dukkan fagen ilmi, musamman a bangaren kimiyya da kere-kere, wato Science and Technology.
Fannonin Ilimi
A tabbace yake cewa kowane fanni na ilmi na da wani nau’i na fa’ida wajen ciyar da ita gaba. Amma al’ummomi sun sha bamban wajen wani fanni ne suka fi bukata wanne ne suke da karancin bukata gare shi. A yayin da mu a nan (wato kasashe masu tasowa) muna da bukatuwar kusan kowane fannin ilmi na zamani sanadiyyar halin da muke ciki, a kasashen da suka ci gaba a fannin tattalin arzikin kasa sai dai su haddade fannonin da suke da nasaka a cikinsa. Wajibi ne a kan kowace al’umma tayi nazari kan al’ummarta, da irin ci gaban da tayi, da abin da take da karancinsa wajen ci gaba a zamanance ne ko a addinance, musamman idan mai addini ce. Bayan wannan nazari ne za ta fahimci nakasarta, da ci gabanta, da fannonin da take da karancin bukatuwa zuwa gare su.
Dangane da abin da ya shafi kasarmu Najeriya a jimlace, da nan Arewacin kasar a takaice, fannin da muka fi tsananin bukata gare shi shi ne fannin kimiyya gaba dayansa. Wannan fanni ne mai fadin gaske, domin ya kunshi likitanci, da fannin lissafi, da kimiyyar sadarwa – da dukkan bangarorinsa – da kuma kere-kere. Duk da shekarun da jami’o’inmu suka kwashe suna karantar da wannan fanni, da himmar da gwamnatoci suka bayar ko suke bayarwa, har yanzu da sauran rina a kaba. Muna da karancin likitoci, da kwararru a fannin sadarwar zamani, da kuma kwararru a fannin kere-kere. Wani abin bakin ma shi ne, duk da karancin kwararru da muke fama da shi a wadannan fannoni, ‘yan kadan din da muke dasu galibi duk sun gudu zuwa wasu kasashe saboda karancin kayan aiki don dabbaka abin da suka koya, ko rashin kula a bangaren hukuma da dai sauran matsaloli da muka sani. Wannan a bangaren wadanda suka kammala karatun kenan.
No comments:
Post a Comment