Like Us On Facebook

Breaking

Monday, August 31, 2020

yyar da kukayi a baya

 

Illa da tasirin da soyayya yake iya yiwa masoya a zuciyar su bayan sun rabu yana da matukar tasiri. Hakan yasa wasu masoyan koda sun rabu saboda yadda suka kasa mantawa da juna, sai kuma su sake dawowa ba tare da la'akari da gyara abunda ya raba su tun a farko ba.
Ba wai mata kadai ba. Hatta maza suna matukar jin jiki idan suka rabu da masoyiya kamin su iya mantawa da ita. Wani lokaci masoya sun fi jin kaunar juna a daidai lokacin da suka rabu da junansu. Hakan yasa sannu a hankali sai kuma a sake ganin su sun sake hadewa an ci gaba da soyayya.
Wani lokacin kuma ba a soyayyar kuma an kasa mantawa da juna. Kullum a begen juna ake da kuma tunanin juna. A wannan darasin zamu kawo muku wasu hanyoyin da tsoffin masoya zasu manta da junansu kamar basu taba rayuwa a baya ba.
Duk wasu masoya da suka rabu kuma suke son su manta da junansu abu na farko da zasu soma dubawa shine abunda ya hadasu suka ɓata.
Muddin abunda ya hadamu kuka samu rashin jituwa bai kai ya kawo ba, to da matukar wahala ku iya rabuwa da juna. Amma idan ka dubi sanadin batawar taku yana da matukar tasiri to daga wannan lokacin zaku soma cire tsammanin juna. Hakan kuma shi zai sa kuyi saurin manta juna ganin matsalar taku ba mai magantuwa bane.
Wata hanyar ta mantawa da tsohuwar soyayya itace ta dace duk wani abun da zai iya tunatar da ku soyayyar ku.
Idan akwai wani kyauta, hotuna, ko wasu alamu da muddin aka gansu za a iya tunawa da juna, a tabbatar da cewa an kauda su ko kuma an salwantar dasu. Hakan zai taimaka wajen mantawa da tsohuwar soyayya.
Toshe duk wasu Hanyoyi na sadarwa a tsakaninku shine hanya na gaba ga masu son su manta da tsohuwar soyayyar data tsaya musu a rai.
Lambar waya, email, ƙafafen sada zumunta na zamani da kuke hira dasu. Dukansu suna bukata a sharesu muddin ana so a daina tuna tsohuwar soyayya.
Kaucewa abokai ko kawaye da kuma duk wanda zai iya tada muku zancen tsohuwar soyayya da kuka bari ya zama dole.
Idan ya zama babu wanda zai zo muku da hiran tsohuwar soyayyar ko kuma yanke mu'amala da duk wani wanda zai kawo zancen abunda ya riga ya wuce, cikin kankanin lokaci zaku ga kun manta da tsohuwar Soyayarnan.
Ku samu wani abunda zai dauke muku hankali da zaku shagaltu dashi nan ma wata hanya ce ta manta da tsohuwar soyayyar data zamemaku halaka kai.
Yin sabuwar budurwa ko saurayi ga masu son mantawa da tsohuwar Soyayarsu shima hanya ce.
Ba lalle bane kuna iya son su kamar yadda kuka so na tsohuwar soyayyar, amma kuma debe kewa da zaku samu anan na iya taimakawa wajen ganin anyi saurin mantawa da tsohuwar soyayya.
Bayan duk anyi waɗannan abubuwan da muka lissafa a sama abu naf gama a kokarin ku na son rabuwa da tunanin tsohuwar soyayya shine a fadawa Allah. Kamar yadda muka sani sau da dama zamu ki abu amma wannan abun ya zama shine alheri a gare mu.
Wani lokacin kuma mu so abu ashe sharri ne a rayuwar mu. Don haka fadawa Allah halin da ake cikin kuma a roƙi Allah Ya yi hukuncin sa daya fi dacewa a tsakanin ku shine abun yi kuma shine yafi dacewa ga masoyan da suka samu sabani kuma sun kasa daina tuna junansu.

No comments:

Post a Comment